"RAYUWA TANA BANI TSORO"

😭😭😭


Idan na tuno lokacin da nake jariri, bana iya komai sai dai ayi mini! Sai nace Allah Shine mai iko🙆🏻


Idan na dubi yadda nake a yanzu, ina iya yiwa kai na abubuwa! Sai nace Alhamdulillahi🙆🏻


Idan na tuno wata rana zan iya tsufa, na koma komai sai dai ayi mini! Sai nace Allah Yasa muyi kyakyawan karshe🙆🏻


Idan na tuno wata rana dole zan bar duniya, da dukiya ta da iyali na duk sai na bar su! Sai nace ashe mutuwa wa'azi ce🙆🏻


Idan na tuno wata rana zan zama gawa, kuma a daukko ni a fitar dani daga cikin gida na! Sai nace ashe rayuwar nan bata da tabbas🙆🏻


Idan na tuno wata rana za a saka ni a cikin wani rami, a karkashin kasa mai duhu babu shimfida! Sai nace ashe ni ba komai bane🙆🏻


Idan na tuno wata rana za a tashe ni a cikin Kabari, domin na amsa wasu tambayoyi! Sai nace ashe Kabari abun tsoro ne🙆🏻


Idan na tuno a lahira za a tsayar dani, domin nayi bayanin abun dana aikata a duniya! Sai nace inama banzo duniyar ba🙆🏻


Idan na tuno irin tashin hankalin da za a fuskanta a ranar lahira! Sai nace dama ba a halicce ni ba🙆🏻


Idan na tuno irin musifar da bala'i dake cikin Wutar Jahannama! Sai nace Allah Yayi mana tsari da ita🙆🏻


Idan na tuna bani da tabbaci na shiga cikin Aljannah! Sai nace Allah Kayi mana Rahamar Ka🙆🏻


Idan na tuno cewa ni  mutum ne mai rauni! Sai nace Allah Ka zama gata na🙆🏻


Ya Allah Kasa mu dace duniya da lahira🙏🏻 

Comments

Popular posts from this blog

FOOD FOR THOUGHT

...JUST BEGIN...

DUNIYA: Wasu darusa daga cikin ta.