DUNIYA: Wasu darusa daga cikin ta.

 Duniya bata taba ce maka 'uffan', amma tafi kowa iya bada darasi, zata gwara mutun nan ta gwara shi can har sai ya gane ina ne ya kamata ya tsaya ina ne ya kamata ya ruga da gudu don gujewa gwarawar ta,

 shi yasa idan kasamu tsofin daliban ta (dattijai) zaka tarar sunfi kowa tsoron ta, da sanin yanda za a zauna cikin ta, ba don komai suka san hakan ba, sai dan yawan gwarasu da tayi yafi na kowa.

Hausawa suka ce wai Duniya ta ishi kowa riga da wando har da babbar riga, kuma wanda bai zoba tana jiran shi. Ita wannan koyarwa da duniya ke mana babu wanda yake tserewa zaman ajinta.

 Amma fa wasu zaman kashe wando suke a ajinta domin  basa fahimtar darasin, masu ganewa sun ji ɗaɗin su waɗanda basa ganewa sukan zo cikin ta suna kuka su koma suna kuka (Allah Ya tsare mu).

Duk mulkinka kana sane da cewar  wani ne ya sauka ka hau, idan kai Sarki ne watakil ma babanka ne ya mutu ka hau mai mulkin siyasa kuwa zaka samu idan ya daga kai a ofishin shi zai haɗa ido da hoton waɗanda suka gabace shi, idan mai fahiimtar karatun duniya ne zai tsaya yayi da kyau kafin tasa shudewar.

Duk gayu da rawar kan matashi akalla koda bai taso ya samu kakansa a raye ba idan ya duba mahaifinsa yasan ba a haka aka haife shi ba duniya ce ta mayar shi haka, idan akwai dalilin da zai hana takai matashin nan inda takai Baba to bai wuce mutuwa ba.

Haka Budurwa ma duk kwalliyar ta da kwalisar ta da gudun kada ace mata tsohuwa toh tasani wata rana itama tsohuwarce.

Ita dai duniya ba zata fasa bada darasi ba wanda yaga zai gane ya gane wanda bazai gane ba ruwan shi amma fa darasin ta babu fasawa...

Comments

Popular posts from this blog

FOOD FOR THOUGHT

...JUST BEGIN...